BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Fannin lafiya na dab da durƙushewa a Gaza - Shugaban WHO
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ''yakin da ake yi a Gaza ya yi mummunar illa ga fannin lafiya''.
Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga a Neja
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta samu nasara halaka wasu 'yan bingida a jihar Naija ciki har da wani gawurtaccen ɗan bindiga da ya jima yana addabar jama'a, mai suna Yellow Jambros.
An hango wani ƙaton rami a kan duniyar rana
Ba a san tsawon lokacin da wannan rami zai ci gaba da kasancewa ba a kan duniyar rana, amma masana kimiyya sun ce irin wadannan ramuka kan iya kasancewa har tsawon juyawa daya na duniya, wato kwana 27.
Waiwaye: Gargaɗin jabun kuɗi da neman biyan diyya kan kisan masu Maulidi a Kaduna
Wannan maƙala na ɗauke da wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata.
Wane irin ciwon ciki ne yake turnuƙe sojojin Isra'ila da suka je yaƙi Gaza?
Wasu sojojin Isra'ila a Gaza na kamuwa da rashin lafiya, inda wani matsanancin ciwon ciki na cutar da ake kira shigella, yake turnuƙe su.
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Matatar man Dangote ta karɓi ɗanyen man fetur a karon farko
Wannan ne kashin farko a cikin ɗanyen mai ganga miliyan shida da matatar ta saye daga manyan kamfanonin haƙo ɗanyen mai.
BBC ta ga bidiyon yadda aka yi wa Falasɗinawa tsirara a Gaza
Wasu hotuna a shafukan sada zumunta sun nuno yadda sojojin Isra'ila suka tsare wasu mutane ba tare da kaya a jikinsu ba a Gaza.
Abin da ya haddasa tashin farashin man zaitun a duniya
Sifaniya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa samar da man zaitun a duniya, inda take samar da kashi 70 na man zaitun da ake amfani da shi a nahiyar Turai, sannan kuma ta samar da kashi 45 na man zaitun ɗin da duniya ke amfani da shi.
'Gwamnati za ta biya diyya ga al’ummar Tudun Biri'
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta biya diyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sanadin harin bam da jirgin saman sojoji ya kai a garin Tudun Biri a jihar Kaduna.
Mutane na tserewa daga Kidandan a Kaduna
Daruruwan jama’a na ci gaba da tserewa daga garin Kidandan da ke karamar hukumar Giwa a jihar kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, sakamakon ƙaruwar hare-haren da ‘yan bindiga da ke ci gaba da kai wa garin.
Hunter Biden na fuskantar tuhuma kan zargin kauce wa biyan haraji
Masu shigara da ƙara na gwamnatin Amurka na tuhumar Hunter Biden kan zargin kauce wa biyan haraji, a karo na biyu da ake tuhumar ɗan shugaban ƙasar da aikata laifi.
Za a hukunta masu hannu a jefa bam kan fararen hula a Tudun Biri - Shettima
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce a shirye gwamnatin tarayya take wajen binciko waɗanda suka jefa bom bisa kuskure a ƙauyen Tudun Biri na ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.
Ko sabon taron dangin jam’iyyun adawa zai tayar da hankalin APC?
Shugaban Jam'iyyar SDP, Shehu Musa Gabam, a jawabin da ya yi wa ƴan jarida bayan taron, ya ce matakin da suka ɗauka wani yunƙuri ne na rage ƙarfin ikon da jam'iyyar APC take da shi a siyasar Najeriya.
Mummunar ambaliyar da ta shafe wani gari a tsakiyar Somaliya
Birnin Beledweyne bai kammala farfaɗowa daga fari mafi muni da ya yi fama da shi ba a cikin shekara 40 sai ga ibtila'in ambaliyar ruwa ta afka masa.
Manyan mutanen da suka yi magana kan jefa wa fararen hula bam a Kaduna
Al'umma da ƴan siyasa da ƙungiyoyin addinin musulunci a Najeriya suna ci gaba da tofa albarkacin bakinsu bayan harin da sojoji suka kai bisa kuskure a Tudun Biri, wani ƙauye a ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna a arewacin ƙasar.
Labaran Bidiyo
Wasanni
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.
Shirye-shiryen rediyo
Nishadi
Shirye-shirye na Musamman
Murya, Me ya sa ba a gabatar wa Kotun Ƙoli sabuwar shaida?Tsawon lokaci, 13,22
Shin kun san abin da ke nufi da asusun ajiyar ƙasashen waje, amfaninsa da kuma irin taimakon da yake yi wa tattalin arzikin ƙasa? A wannan shiri - wanda Badamasi Abdulkadir Muktar ya gabatar - an kuma amsa tambaya kan gabatar da sabuwar shaida a Kotun Koli.
Murya, Gane Mini Hanya: Kan matsalar wutar lantarki a NajeriyaTsawon lokaci, 11,56
Wani abu da ke ɗaurewa ‘yan Najeriya kai shi ne yadda har yanzu kasar ba ta fi ƙarfin wutar lantarkin da za ta wadatar da al’ummarta ba duk kuwa da cewa ta kwashe fiye da shekara 60 da samun ‘yancin kai.
Murya, Ra'ayi Riga: Hari kan fararen hula bisa kuskure a Tudun BiriTsawon lokaci, 59,33
Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon ya duba harin jirgin sojojin Najeriya kan masu Maulidi a garin Tudun Biri, wanda hukumomi suka ce 'kuskure' ne. Me ya kamata a yi don bi wa waɗannan mutane haƙƙinsu, kuma waɗanne matakai ya kamata a ɗauka domin hana sake faruwar hakan?
Kimiyya da Fasaha
Hotuna
Shafukan Sada Zumunta
Wanda aka fi karantawa
Cikakkun Rahotanni
'An yi min auren dole ina da shekara 12'
An aurar da Tamara lokacin tana da shekara 12 d haihuwa, ta haihu tana da shekara 13 - ana aurar da yara miliyan ɗaya a faɗin duniya kafin su kai shekara 18.
'Kasafin kuɗin da Tinubu ya gabatar cike yake da bashi da yaudara'
Kasafin da Tinubu ya yi wa laƙabi da "kasafin sabunta fata", an gina shi kan hasashen farashin gangar ɗanyen mai dala 96, kuma gwamnati na fatan samar da gangar danyen mai miliyan ɗaya da dubu 78 a kowace rana, yayin da musayar dala ɗaya za ta kasance kan naira 750.
'Ba na son na haifi ƴaƴa saboda tsoron sauyin yanayi'
Wasu mata a Najeriya, da Brazil, da Nepal sun yi bayanin dalilin da ya sa ba su son haihuwa saboda sauyin yanayi, da kuma yadda suke fama da matsin lamba daga al'umma.